Yaushe Lamine Yamal ya fara cin hat-trick idan aka kwatanta da Messi da Ronaldo?

Matashin ɗan wasan Lamine Yamal na FC Barcelona yaci hat-trick na farko a rayuwarsa ta ƙwallo. Amma tambaya ita ce yaushe Lionel Messi da Cristiano Ronaldo suka fara yin hakan?
Dan wasan mai shekaru 18 ya zura kwallaye uku cikin nasarar da Barcelona ta samu da ci 4-1 a kan Villarreal CF, sakamakon da yasa kungiyar ke cigaba da jan ragamar gasar La Liga.
Yamal ya zura kwallaye biyu a farkon rabin lokaci na farko, duk daga taimakon abokan wasansa wanda suka fito tare daga makarantar matasa ta La Masia, wato Fermin Lopez. Daga baya ya kammala hat-trick dinsa a tsakiyar rabin lokaci na biyu.
Yanzu haka Yamal shi ne na uku mafi karancin shekaru a tarihin La Liga da ya taba cin hat-trick, kuma shi ne na farko a zamanin bayan Yaƙin Duniya na Biyu da ya cimma wannan nasara.
Yan wasan biyu kacal ne suka taba yin hakan suna kasa da shekarunsa
- Jose Iraragorri (shekaru 17 da kwana 337) a 1930
- Pombo (shekaru 18 da kwana 200) a 1934
Yamal ya bayyana cewa
Ban ji dadi sosai ba a farkon kakar wasa. Na samu matsalar mara (groin), kuma ban kasance cikin farin ciki ba. Amma yanzu na fi jin dadi, ina murmushi idan ina wasa, kuma ina jin dadi a filin wasa.
Hat-trick dinsa na farko ya kara zama wani babban mataki a rayuwarsa ta ƙwallo.
Amma ga yadda abin ya kasance ga Messi da Ronaldo
Lamine Yamal Hat-trick na Farko
-
A wasan Barcelona 4-1 Villarreal
-
Rana: 28 Fabrairu 2026
-
Shekara: 18, wata 7, kwana 15
-
Lokaci tun bayan fara wasansa na farko: Shekara 2, wata 9, kwana 30
-
Jimillar wasanni kafin hat-trick: 163
Lionel Messi Hat-trick na Farko
-
Wasan Barcelona 3-3 Real Madrid
-
Rana: 10 Maris 2007
-
Shekara: 19, wata 8, kwana 14
-
Lokaci tun bayan fara wasansa na farko: Shekara 2, wata 4, kwana 22
-
Jimillar wasanni kafin hat-trick: 69
Cristiano Ronaldo Hat-trick na Farko
- Wasan Manchester United 6-0 Newcastle United
- Rana: 12 Janairu 2008
- Shekara: 22, wata 11, kwana 7
- Lokaci tun bayan fara wasansa na farko: Shekara 5, wata 4, kwana 29
- Jimillar wasanni kafin hat-trick: 299
Kwatantawa a Taƙaice
Yamal yayi hat-trick dinsa yana ƙasa da shekarun Messi da Ronaldo.
Messi yayi nasa cikin ƙananan wasanni (69).
Ronaldo ya dauki lokaci mafi tsawo kafin ya fara yin hat-trick.
Wannan ya nuna yadda Yamal ke tafiya cikin sauri a farkon rayuwarsa ta ƙwallo.








