Messi Da Argentina Sun Zaɓi Kansas City Amurka A Matsayin Mazauni A Kofin Duniya 2026

Shirye-shiryen Gasar Kofin Duniya ta 2026 na ƙara ɗaukar sabon salo yayin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Argentina ta sanar da zaɓen birnin Kansas City, jihar Missouri (USA) a matsayin babbar hedkwatar su (home base) a lokacin gasar.
Wannan sanarwa ta fito ne a ranar Laraba, inda hukumar ƙwallon ƙafar Argentina (AFA) ta bayyana cewa Kansas City za ta kasance cibiyar da yan wasan Argentina, ciki har da Lionel Messi, zasu zauna, su yi atisaye, tare da shirin fuskantar wasannin gasar a lokacin bazarar 2026.
Argentina zata je world cup 2026 a matsayin zakaran duniya

Argentina na zuwa gasar ta 2026 ne a matsayin zakarun duniya masu kare kambunsu, bayan lashe Kofin Duniya a Qatar 2022. Burin ƙungiyar shi ne ta zama ƙasa ta farko cikin fiye da shekaru 50 da za ta iya lashe Kofin Duniya sau biyu a jere.
Idan har Argentina ta ɗaga kofin a shekarar 2026, hakan zai sa ta rage tazarar da ke tsakaninta da babbar abokiyar hamayyarta Brazil, wacce ke riƙe da mafi yawan kofuna a tarihin gasar. Wannan nasara kuma za ta ƙara ƙarfafa matsayin Argentina a tarihin ƙwallon ƙafa na duniya.
Messi a gaba, Argentina na daga cikin manyan yan takara
Yayin da Lionel Messi ke shirin sake jagorantar ƙungiyar ƙarƙashin koci Lionel Scaloni, mutane da dama na kallon Argentina a matsayin babbar ƙungiya da aka fi bai wa damar lashe gasar, musamman ganin cewa gasar 2026 za ta kasance ta farko da ƙungiyoyi 48 za su shiga.
Ƙwarewa, haɗin kai, da gogewar da Argentina ta samu a manyan gasa na baya yasa ake kallonta a matsayin ƙungiya mai cikakken shiri.
Dalilin da yasa Argentina ta zaɓi Kansas City

A wata sanarwa da hukumar AFA ta fitar, ta bayyana cewa an yanke shawarar zaɓen Kansas City ne bayan ziyara da bincike da dama da jami’ai da masu kula da lafiyar yan wasa suka gudanar.
A cewar AFA
Bayan jerin bincike da rahotanni masu zurfi daga masu horar da jiki da jami’an gudanarwa, mun yanke hukuncin cewa Kansas City ita ce wuri mafi dacewa domin fuskantar gasar, musamman duba da tazara tsakanin biranen da kuma sauƙin abubuwan more rayuwa ga tawagar baki ɗaya.
Kasancewar Kansas City na tsakiyar Amurka, hakan zai taimaka matuƙa wajen rage wahalar tafiye-tafiye, wani muhimmin abu ganin cewa gasar 2026 za a gudanar da ita ne a ƙasashe uku: Amurka, Kanada da Mexico.
Filin wasan farko da wuraren atisaye
Duk da cewa har yanzu ba a bayyana cikakken filin atisayen da Argentina zata yi amfani da shi ba, an riga an tabbatar da cewa filin Arrowhead Stadium, wanda shi ne gidan ƙungiyar NFL ta Kansas City Chiefs, zai karɓi wasan farko na Argentina a gasar 2026.
Wannan filin wasa na daga cikin manyan filayen wasanni a Amurka, kuma yana da ƙwarewa wajen karɓar manyan abubuwan wasanni na duniya.
Ƙungiyoyin da Argentina za ta fuskanta a zagayen rukuni
Argentina na cikin Rukuni J (Group J) a gasar Kofin Duniya ta 2026, inda za ta fafata da:
- Algeria
- Austria
- Jordan
Jadawalin wasannin Argentina a Group Stage
16 ga Yuni, 2026: Argentina vs Algeria a Arrowhead Stadium, Kansas City
22 ga Yuni, 2026: Argentina vs Austria a AT&T Stadium, Arlington, Texas
27 ga Yuni, 2026: Argentina vs Jordan a AT&T Stadium, Arlington, Texas
Sakamakon waɗannan wasanni ne zai yanke hukuncin inda Argentina zata buga wasanninta na gaba a matakan knockout.
Babban buri: wasan ƙarshe a MetLife Stadium
Ko da yake har yanzu hanya na cike da ƙalubale, burin Argentina a bayyane yake kaiwa wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2026, wanda za’a buga a ranar 19 ga Yuli, 2026 a MetLife Stadium, East Rutherford, New Jersey.
Tawagar zata isa Kansas City tun kafin fara gasar, tare da cikakken shiri da manufa ɗaya: kare kambunta da rubuta sabon tarihi.
Zaɓen Kansas City a matsayin hedkwata ya nuna irin shirin da Argentina ke yi domin gasar Kofin Duniya ta 2026. Tare da Messi, gogaggen koci Scaloni, da ƙungiya mai cike da ƙwarewa, La Albiceleste na shirin fuskantar gasar da cikakken kwarin gwiwa.
Masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya na jiran ganin ko Argentina zata iya sake maimaita abin da tayi a 2022, ko kuwa sabbin ƙalubale zasu hana ta cimma burinta.








