Labarin Wasanni

Lamine Yamal Ya Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasan La Liga, Amma Sau Nawa Messi Da Cristiano Ronaldo Suka Ci?

Lamine Yamal ya sake rubuta tarihi bayan da ya lashe kyautar Gwarzon Dan Wasan La Liga na kakar 2025/26, lamarin da ya kara tabbatar da cewa tauraron Barcelona yana cikin manyan yan wasan duniya duk da karancin shekarunsa.

La Liga ta sanar da hakan a hukumance ranar Juma’a, inda ta bayyana cewa matashin dan wasan mai shekaru 18 yafi sauran yan takarar kyautar haskakawa a kakar da ta gabata.

Lamine Yamal Ya Doke Manyan Yan Takara

A cikin jerin yan wasan da suka fafata domin samun kyautar, akwai tauraron Real Madrid Kylian Mbappe, wanda yazo na biyu bayan kakar da ya taka rawar gani duk da matsalolin rauni da kuma rashin kofuna.

Sauran yan takarar sun hada da Nicolas Pepe na Villarreal, Vedat Muriqi na Mallorca da kuma Pablo Fornals na Real Betis.

A kakar bana, Lamine Yamal ya zura kwallaye 16 sannan ya bayar da assists 12 cikin wasanni 28 da ya buga, wanda ke nuna cewa ya samar da gudunmawar kwallo guda daya a kusan kowane wasa.

Duk da ya fuskanci matsalolin rauni a wasu lokuta na kakar wasa, Yamal ya kasance babban makamin kai hari na Barcelona, musamman lokacin da Robert Lewandowski da Raphinha suka yi jinya.

Yamal Ya Kafa Sabon Tarihi A La Liga

Kafin wannan nasara, Lamine Yamal ya taba lashe kyautar Mafi Kyawun Dan Wasa Matashi (U-23) ta La Liga a shekarun 2024 da 2025.

Yanzu kuma ya dauki babban mataki ta hanyar zama mafi karancin shekaru da ya taba lashe kyautar Gwarzon Dan Wasan La Liga.

Da wannan nasara, Yamal ya karya tarihin da Lionel Messi ya kafa. Messi ya fara lashe kyautar ne yana da shekaru 21 bayan kakar 2008/09.

Sau Nawa Lionel Messi Ya Lashe Kyautar?

Duk da nasarar da Yamal ya samu, har yanzu yana da doguwar hanya kafin ya kai matsayin Messi.

Tsohon tauraron Barcelona din ne ke rike da tarihin lashe kyautar Gwarzon Dan Wasan La Liga sau tara.

Messi ya lashe kyautar a shekarun:

  • 2009
  • 2010
  • 2011
  • 2012
  • 2013
  • 2015
  • 2017
  • 2018
  • 2019

Har ila yau, Messi ya lashe kyautar sau biyar a jere, abin da babu wani dan wasa da ya taba yi a tarihin gasar.

Yaya Tarihin Cristiano Ronaldo?

Duk da irin nasarorin da ya samu tare da Real Madrid, Cristiano Ronaldo bai samu damar mamaye kyautar kamar yadda Messi ya yi ba.

Tauraron Portugal din ya lashe kyautar Gwarzon Dan Wasan La Liga sau daya kacal a tsawon shekaru tara da ya shafe yana taka leda a Spain.

Ronaldo ya samu wannan gagarumar karramawa ne a shekarar 2014.

Shin Lamine Yamal Zai Iya Kaiwa Tarihin Messi?

A halin yanzu, Lamine Yamal yana daya daga cikin manyan yan wasan da ake sa ran zasu mamaye kwallon kafa na shekaru masu zuwa.

Da shekaru 18 kacal, ya riga ya kafa tarihin zama mafi karancin shekaru da ya lashe kyautar Gwarzon Dan Wasan La Liga. Idan ya ci gaba da irin wannan bajintar, akwai yiwuwar ya kusanci tarihin Lionel Messi a nan gaba.

Leave a Reply

Related Articles