Yan Wasa 100 Mafi Tsada A Duniya 2025/26: Yamal Da Haaland Suna Cikin Jerin, Mbappe Yana Ciki

Yan Wasa Mafi Tsada A Duniya sun sake jan hankalin masoya kwallon kafa bayan Transfermarkt ta fitar da sabon jadawalin kimar yan wasa bayan kammala kakar wasa ta 2025/26.
Yayin da aka rufe kakar wasa da wasan karshe na Champions League, hankalin duniya ya koma gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026. Wannan ya sa Transfermarkt ta sabunta kimar dubban yan wasa daga manyan lig-lig na duniya domin tantance wadanda suka fi daraja a kasuwar kwallon kafa.
Su Waye Yan Wasan Da Suka Fi Tsada A Duniya?
Tauraron Barcelona Lamine Yamal da dan wasan Manchester City Erling Haaland ne suka mamaye saman jadawalin, inda kowannensu ke da kimar kasuwa ta euro miliyan 200.
Duk da cewa suna da kima iri daya, an sanya Yamal a matsayi na farko saboda yana da karancin shekaru fiye da Haaland.
Matashin dan wasan Barcelona ya taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa kungiyar lashe La Liga, inda ya samar da kwallaye da assists guda 42 a dukkan gasa.
A bangaren Haaland kuwa, ya ci kwallaye 38 cikin wasanni 52 da ya bugawa Manchester City a kakar bana.
Mbappe Ya Sauka Zuwa Matsayi Na Uku
Tauraron Real Madrid Kylian Mbappe, wanda a baya yake da kimar euro miliyan 200 kamar Yamal da Haaland, ya fuskanci raguwar kima da euro miliyan 20.
Sabuwar kimarsa yanzu ta kai euro miliyan 180, wanda ya sanya shi a matsayi na uku cikin yan wasa mafi tsada a duniya.
Duk da ya ci kwallaye 42 a wasanni 44, rashin manyan kofuna tare da wasu dalilai na shekaru da abubuwan da suka shafi harkokinsa a wajen fili sun taimaka wajen rage kimarsa.
Manyan Biyar Mafi Tsada A Duniya
Jerin manyan ‘yan wasa biyar mafi tsada a duniya ya hada da:
- Lamine Yamal (€200m)
- Erling Haaland (€200m)
- Kylian Mbappe (€180m)
- Michael Olise (€150m)
- Pedri (€150m)
Dukkaninsu suna cikin fitattun ‘yan wasan da suka haskaka a kakar 2025/26.
PSG Ta Mallaki Tawaga Mafi Tsada A Duniya

Bayan nasarorin da PSG ta samu a Turai, kungiyar yanzu tana da tawaga mafi tsada a duniya.
Sabbin kimomin sun nuna cewa ‘yan wasa irin su Joao Neves, Khvicha Kvaratskhelia da Vitinha suna cikin manyan ‘yan wasa goma mafi tsada a duniya.
Hakan ya kara nuna irin ci gaban da PSG ta samu a shekarun baya-bayan nan.
Declan Rice Ya Fi Kowa Tsada A Arsenal
Duk da cewa Premier League ita ce gasar da ta fi kowacce daraja a duniya, Haaland ne kadai dan wasan gasar da yake cikin manyan goma.
Tauraron Arsenal Declan Rice ne ke biye da shi a cikin ‘yan wasan Ingila mafi tsada, inda kimarsa ta kai euro miliyan 120.
Rice yana matsayi na 12 a duniya bayan bajintar da ya nuna tare da Arsenal a kakar bana.








