Yan Wasan Kwallon Kafa 10 Da Ya Kamata Ku Kalla A Kofin Duniya 2026

Yan Wasan Kwallon Kafa 10 da zasu ɗauki hankalin duniya a gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026 sun haɗa da manyan taurarin ƙwallon ƙafa da kuma sababbin hazikai masu tasowa. Daga fitattun gwaraza zuwa matasan dake kafa tarihi, masoya ƙwallon ƙafa zasu samu abin kallo mai ban sha’awa a wannan gasa.
Yayin da gasar ke gabatowa, akwai wasu sunaye da ake sa ran za su mamaye kanun labarai saboda bajintarsu da tasirinsu a filin wasa. Ga jerin fitattun taurarin da ya kamata ku sa ido a kansu.
Taurarin Da Za Su Haskaka Kofin Duniya 2026
Lionel Messi (Argentina)

Lionel Messi zai buga gasar Kofin Duniya karo na shida a tarihinsa, abinda zai daidaita tarihin mafi yawan halartar gasar. Duk da shekaru 38 da yake dasu, har yanzu shi ne zuciyar wasan Argentina kuma babban abin fata wajen kare kambun da suka lashe a Qatar 2022.
Lamine Yamal (Spain)

Lamine Yamal yana cikin mafi kyawun matasan yan wasa a duniya a halin yanzu. Bayan taimakawa Spain lashe Euro 2024, yanzu zai fara buga Kofin Duniya karo na farko, inda ake sa ran zai nuna bajintarsa a idon duniya.
Kylian Mbappe (France)

Kylian Mbappe ya shiga gasar ne bayan ya kafa kansa a matsayin ɗaya daga cikin mafi hatsarin yan wasan gaba a duniya. Bayan lashe Golden Boot a Kofin Duniya na 2022, yana son jagorantar Faransa zuwa sabon kambun duniya.
Erling Haaland (Norway)

Erling Haaland zai fara buga Kofin Duniya a rayuwarsa bayan ya taimaka wa Norway samun gurbin shiga gasar. Dan wasan Manchester City ya kasance daya daga cikin mafi yawan zura kwallaye a duniya cikin yan shekarun nan.
Cristiano Ronaldo (Portugal)

Cristiano Ronaldo na iya buga Kofin Duniya na ƙarshe a rayuwarsa. Duk da cewa yanzu yana da shekaru 41, har yanzu yana daga cikin fitattun yan wasan da zasu ja hankalin miliyoyin masoya ƙwallon ƙafa.
Harry Kane (England)

Harry Kane zai jagoranci Ingila a matsayin kyaftin kuma babban mai zura kwallaye. Tauraron Bayern Munich yana son sake lashe kyautar Golden Boot kamar yadda yayi a shekarar 2018.
Vinicius Junior (Brazil)

Vinicius Junior ya zama ɗaya daga cikin manyan taurarin duniya bayan nasarorin da ya samu tare da Real Madrid. Gudunsa, dribbling da kwarewarsa zasu zama babban makami ga Brazil.
Antoine Semenyo (Ghana)

Antoine Semenyo yana cikin yan wasan da ake sa ran zasu haskaka gasar. Dan wasan Ghana ya nuna kwarewa sosai a kakar wasan da ta gabata kuma yanzu ya zama daya daga cikin jagororin tawagarsa.
Arda Guler (Turkiye)

Arda Guler ya riga ya zama sananne a Turai duk da ƙuruciyarsa. Tauraron Real Madrid yana da damar bayyana kansa a duniya baki ɗaya a wannan gasar.
Mohamed Salah (Egypt)

Mohamed Salah yana cikin manyan yan wasan Afirka na kowane zamani. Duk da nasarorin da ya samu tare da Liverpool, har yanzu yana neman babban nasara tare da ƙasarsa ta Masar.
Waɗanne Ne Zasu Fi Haskakawa?
Kofin Duniya na 2026 zai haɗa tsofaffin gwaraza da sababbin taurari a gasa guda. Yayin da wasu ke neman kammala tarihi, wasu kuma suna neman fara sabon babi a rayuwarsu. Wannan ne ya sa ake sa ran gasar za ta kasance ɗaya daga cikin mafi kayatarwa a tarihin ƙwallon ƙafa.








