Labarin Wasanni

Real Madrid Na Shirin Tura Tayin €150m Ga Wani Matashin Tauraro, Perez Ya Bayar Da Karin Bayanai

Tayin €150m da Real Madrid ke shirin mikawa domin daukar wani babban dan wasa ya jawo ce-ce-ku-ce a duniyar kwallon kafa bayan shugaban kungiyar, Florentino Perez, ya bayyana wasu muhimman bayanai game da shirin.

A wata sanarwa mai daukar hankali, Perez ya tabbatar cewa Real Madrid za ta aike da tayin Euro miliyan 150 a hukumance domin daukar wani babban tauraro da yake cikin matasa masu tasowa a duniya.

“Zai kasance tayin Euro miliyan 150 a hukumance domin wani babban dan wasa. Za mu aika da tayin ranar Talata,” in ji Perez.

Ba Michael Olise Bane

Screenshot 20260605 085912

Duk da rade-radin da suka yadu, Perez ya musanta cewa dan wasan da ake nufi shi ne Michael Olise.

Shugaban na Madrid ya bayyana cewa Olise babban dan wasa ne, amma ba shi ne dan wasan da kungiyar ke shirin kashe Euro miliyan 150 domin siya ba.

Ba Erling Haaland Ko Harry Kane Ba Ne

Screenshot 20260605 090002

Haka kuma Perez ya kawar da jita-jitar dake danganta tayin da Erling Haaland. Duk da kasancewar tauraron dan wasan daya daga cikin fitattun yan wasa a duniya, shugaban Madrid ya ce ba shi ne dan wasan da ake nufi ba.

Screenshot 20260605 090013

Hakazalika ya tabbatar cewa ba Harry Kane bane, yana mai jaddada cewa dan wasan da ake son dauka ba ya buga wasa a gasar Premier League.

Dan Wasan Matashi Ne Mai Matsayin Galactico

Perez ya kara bayyana cewa dan wasan da ake son siya matashi ne kuma yana da matakin da zai iya zama sabon Galactico a Real Madrid.

1780645973732

Ya kwatanta dan wasan da fitattun taurari irin su Cristiano Ronaldo da Kaka, wadanda suka taba zama manyan Galacticos bayan komawarsu Santiago Bernabeu.

“Dan wasa ne mai matukar hazaka kuma yana da matakin Galactico kamar Cristiano da Kaka,” in ji shugaban na Madrid.

Wanene Dan Wasan?

Duk da wadannan bayanai, Perez bai bayyana sunan dan wasan ba, lamarin da ya kara sanya magoya baya cikin tunani da hasashe.

Tunda ya tabbatar cewa ba dan wasan Premier League bane kuma matashi ne, hankula sun fara karkata zuwa wasu daga cikin fitattun matasan taurarin Turai da ke haskakawa a halin yanzu.

Har yanzu dai babu tabbacin sunan dan wasan, amma idan Real Madrid ta tura tayin Euro miliyan 150 kamar yadda aka sanar, hakan na iya zama daya daga cikin manyan cinikayyar da za su girgiza kasuwar musayar yan wasa a wannan shekarar.

Leave a Reply

Related Articles