Tarihi

Tarihin Diego Maradona Gwarzon Da Ya Sauya Duniya Ta Kwallon Kafa

Tarihin Diego Maradona

Diego Maradona yana daga cikin manyan yan wasan ƙwallon ƙafa mafiya tasiri a tarihin duniya. Mutane da dama suna kallonsa a matsayin daya daga cikin mafi hazaka da kwarewa da aka taba gani a harkar ƙwallon ƙafa.

An haifi Diego Armando Maradona ranar 30 ga Oktoba, 1960 a Lanús dake Buenos Aires na kasar Argentina. Ya taso cikin talauci amma hakan bai hana shi nuna baiwar da Allah ya ba shi ba tun yana ƙarami.

Maradona ya fara jawo hankalin duniya tun yana yaro saboda kwarewarsa wajen dribbling, passing da kuma sarrafa ƙwallo cikin sauƙi.

Yadda Maradona Ya Fara Kwallo

Diego Maradona ya fara buga ƙwallo a kungiyar matasa ta Argentinos Juniors.

Yana da shekaru 15 kacal lokacin da ya fara buga wasan ƙwararru, lamarin da ya sa ya zama daya daga cikin matasan da suka fi daukar hankali a Argentina a lokacin.

Bayan wasu shekaru masu kyau, ya koma Boca Juniors, kungiyar da yake matukar so tun yana karami.

A Boca Juniors ne Maradona ya kara samun farin jini kafin daga baya ya koma Turai.

Komawarsa FC Barcelona

A shekarar 1982, FC Barcelona ta sayi Maradona a lokacin da ya zama daya daga cikin mafi tsadar ‘yan wasa a duniya.

Duk da cewa ya nuna bajinta sosai a Spain, ya sha fama da raunuka da kuma matsaloli a wasu lokuta.

Duk da haka, ya taimaka wa Barcelona wajen lashe Copa del Rey da wasu manyan kofuna.

Lokacin Zinare A Napoli

Bayan barin Barcelona, Diego Maradona ya koma Napoli a shekarar 1984.

Wannan lokaci ne da ya canza tarihin kungiyar gaba daya.

Kafin zuwan Maradona, Napoli ba ta daga cikin manyan kungiyoyin Italy. Amma bayan zuwansa, kungiyar ta zama daya daga cikin mafi ƙarfi a Serie A.

Maradona ya taimaka wa Napoli wajen lashe:

  • Serie A sau biyu
  • Coppa Italia
  • UEFA Cup
  • Italian Super Cup

Har yanzu magoya bayan Napoli suna kallonsa a matsayin gwarzon da ya sauya tarihin kungiyar.

Maradona Da Kofin Duniya Na 1986

Abin da ya fi sanya Diego Maradona cikin tarihin duniya shi ne abin da ya yi a FIFA World Cup na 1986.

Ya jagoranci Argentina zuwa lashe kofin duniya bayan nuna bajinta mai ban mamaki.

A wasan quarter final da Ingila, Maradona ya ci daya daga cikin kwallayen da suka fi shahara a tarihi.

Na farko shine kwallon “Hand of God” inda ya taba ƙwallo da hannu kafin ta shiga raga.

Bayan mintuna kadan kuma yaci wata kwallo ta musamman bayan yayi dribble daga tsakiyar fili ya wuce kusan dukkan yan wasan Ingila.

Wannan kwallo har yanzu ana kallonta a matsayin daya daga cikin mafi kyawun goals a tarihin ƙwallon ƙafa.

Salon Wasan Maradona

Diego Maradona ya shahara wajen:

  • Dribbling
  • Passing
  • Vision
  • Free kicks
  • Leadership

Mutane da yawa suna kwatanta kwarewarsa da irin ta Lionel Messi saboda yadda yake sarrafa ƙwallo.

Duk da cewa ba shi da tsayi sosai, yana da balance da control mai ban mamaki.

Kyaututtuka Da Nasarorin Maradona

Kyauta Ko Nasara Shekara
FIFA World Cup 1986
FIFA World Cup Golden Ball 1986
Serie A Champion 1987, 1990
UEFA Cup 1989
FIFA Player Of The 20th Century 2000

Matsalolin Da Ya Fuskanta

Duk da bajintarsa, Maradona ya sha fama da matsaloli a rayuwarsa.

Ya fuskanci matsalar shaye-shaye da kuma cece-kuce da dama a harkar ƙwallo.

Wadannan matsaloli sun shafi rayuwarsa da kuma aikinsa a wasu lokuta.

Duk da haka, hakan bai rage matsayin da yake da shi a tarihin ƙwallon ƙafa ba.

Mutuwar Maradona

Diego Maradona ya rasu ranar 25 ga Nuwamba, 2020 yana da shekaru 60.

Mutuwarsa ta girgiza duniyar ƙwallon ƙafa gaba daya, inda miliyoyin mutane suka nuna alhini.

Kasashen duniya da manyan kungiyoyi sun yi masa girmamawa saboda irin gudunmawar da ya bayar a wasanni.

Gadon Da Maradona Ya Bari

Har yanzu Diego Maradona yana daga cikin sunayen da ba za a manta da su ba a tarihin ƙwallon ƙafa.

Salon wasansa, jajircewarsa da kuma yadda ya faranta ran magoya baya sun sa ya zama gwarzo na har abada.

Ga magoya bayan Argentina da Napoli musamman, Maradona ba kawai tsohon dan wasa ba ne, alama ce ta tarihin ƙwallon ƙafa.

Leave a Reply