Sharhi

Jerin Yan Wasan Da Suka Fi Karbar Kudi A Duniya Kasa Da Shekaru 25 A 2026

Duniyar wasanni ta zamani na cigaba da samar da matasa masu tarin arziki tun kafin su kai shekaru 25.

Daga ƙwallon ƙafa zuwa kwallon kwando da tennis, sababbin taurari suna samun dimbin kudade daga albashi, sponsorships da sauran harkokin kasuwanci.

A shekarar 2026, manyan yan wasa daga kungiyoyi irin su Manchester City, Real Madrid da NBA sun shiga cikin jerin matasan da suka fi karbar kudi a duniya.

Ga cikakken jerin manyan taurarin wasanni masu shekaru 25 ko kasa da haka da suka fi samun kudade a duniya.

6. Jannik Sinner – Dala Miliyan 54.6

0X0 6

Tauraron tennis na kasar Italiya yana daya daga cikin fitattun yan wasa a ATP rankings.

Jannik Sinner ya cigaba da kafa tarihi bayan zama dan wasa na biyu bayan Novak Djokovic da ya lashe dukkan ATP Masters 1000.

Baya ga nasarorin tennis, yana samun kudade masu yawa daga partnerships da manyan kamfanoni.

5. Cade Cunningham – Dala Miliyan 58.6

0X0 5

Tauraron Detroit Pistons ya nuna babban cigaba a NBA.

Cade Cunningham ya taimaka wa kungiyarsa wajen samun daya daga cikin mafi kyawun records a Eastern Conference.

Har ila yau yana da sponsors masu yawa da suka hada da Ford da State Farm.

4. Vinicius Junior – Dala Miliyan 60

0X0 4

Vinicius Junior yana daya daga cikin fitattun taurarin ƙwallon ƙafa a duniya yanzu.

Tauraron Brazil din ya lashe kyautar Best FIFA Men’s Player ta 2024 kuma ya kasance daya daga cikin mafi tasiri a La Liga cikin shekaru biyar da suka gabata.

Baya ga albashinsa a Real Madrid, Vinicius yana samun kudade daga manyan brands irin su Hugo Boss da Rexona.

3. Carlos Alcaraz – Dala Miliyan 61.5

0X0 3

Dan wasan tennis na Spain yana daya daga cikin mafi kayatarwa a duniya.

Carlos Alcaraz ya lashe manyan gasar Grand Slam guda uku cikin shekara daya, lamarin da ya kara masa farin jini sosai.

Rikicinsa da Jannik Sinner na cigaba da zama daya daga cikin manyan rivalries a tennis.

Alcaraz yana samun kudade masu yawa daga endorsement deals da kuma exhibition matches.

2. Anthony Edwards – Dala Miliyan 69

0X0 2

Tauraron Minnesota Timberwolves ya zama daya daga cikin manyan sunaye a NBA.

Anthony Edwards ya kara shahara bayan lashe NBA All-Star Game MVP da kuma sakin album dinsa na waka.

Haka kuma yana da manyan sponsorship deals da suka hada da Adidas da Prada.

1. Erling Haaland – Dala Miliyan 80

0X0 1

Erling Haaland shi ne matashin dan wasa mafi yawan kudi a duniya a shekarar 2026.

Tauraron Manchester City ya samu kusan dala miliyan 80 daga albashi da kuma endorsement deals a cikin watanni 12.

Dan wasan Norway din ya cigaba da kafa tarihi a Premier League da UEFA Champions League.

Haaland ya zama dan wasa mafi saurin kaiwa kwallaye 50 a Champions League sannan kuma ya kafa sabon tarihi wajen kaiwa goals 100 a Premier League cikin sauri.

Baya ga harkar ƙwallo, yana da sponsorships da manyan kamfanoni irin su Nike da Dolce & Gabbana.

Matasan Taurari Sun Mamaye Wasanni

Abin lura shi ne yadda matasa suke kara mamaye jerin manyan masu kudi a wasanni.

Yan wasa masu shekaru a 20s yanzu sun fi wadanda suka haura shekaru 30 yawa a cikin manyan athletes masu karbar kudi a duniya.

Hakan na nuna yadda sababbin taurari suke samun manyan contracts da sponsorships tun suna kanana.

Kammalawa

Daga ƙwallon ƙafa zuwa tennis da NBA, shekarar 2026 ta nuna cewa matasa suna cigaba da zama manyan taurari a harkar wasanni.

Duk da kasancewar akwai manyan gogaggun yan wasa a duniya, sababbin taurari irin su Haaland, Vinicius Junior da Carlos Alcaraz sun nuna cewa su ne makomar wasanni.

Kuma da alama wannan jerin zai kara canzawa yayin da sababbin matasa ke ci gaba da bayyana a duniya.

Leave a Reply

Related Articles