Kungiyoyin Da Suka Fi Tura Yan Wasan Su Zuwa FIFA World Cup 2026

Yayin da ake shirin fara gasar FIFA World Cup 2026, an bayyana jerin kungiyoyin da suka fi yawan ‘yan wasan da za su wakilci kasashensu a gasar. Wannan ya nuna irin gudunmawar da manyan kungiyoyin duniya ke bayarwa wajen samar da fitattun ‘yan wasa ga tawagogin kasa.
A saman jerin akwai Manchester City, wadda za ta samu ‘yan wasa 19 da suka buga wasansu na karshe a matakin kungiya tare da ita kafin shiga sansanonin kasashensu domin gasar kofin duniya.
Wannan adadi ba wai shi ne mafi yawa a Ingila kadai ba, har ma shi ne mafi girma a duk duniya kafin fara gasar ta 2026.
A dunkule, akwai kungiyoyi 17 da suka samu akalla ‘yan wasa 10 ko sama da haka a gasar kofin duniya ta bana. Daga cikinsu, kungiyoyi biyar sun fito ne daga gasar Premier League ta Ingila.
Manchester City Na Kan Gaba
Manchester City ce ke jagorantar wannan jerin da ‘yan wasa 19, lamarin da ke nuna zurfin ingancin tawagarta da kuma yadda take cike da fitattun ‘yan wasa daga kasashe daban-daban.
A matsayi na biyu akwai Bayern Munich da yan wasa 18, yayin da Arsenal da Paris Saint-Germain ke biye da ‘yan wasa 17 kowacce.
Barcelona ce ta kammala manyan kungiyoyi biyar na farko da yan wasa 15 da zasu halarci gasar.
Sauran Kungiyoyin Da Suka Yi Fice
Kungiyoyin Crystal Palace, Manchester United, Al-Hilal da Atletico Madrid duk suna da ‘yan wasa 12 da za su shiga gasar.
Haka kuma Liverpool, Borussia Dortmund da Galatasaray suna da ‘yan wasa 11 kowacce.
Sauran kungiyoyin da suka samu ‘yan wasa 10 a gasar sun hada da Slavia Prague, AC Milan, PSV Eindhoven, Real Madrid da Fenerbahce.
Jerin Kungiyoyin Da Suka Fi Tura Yan Wasa Zuwa Kofin Duniya Ta 2026
| Kungiya | Adadin ‘Yan Wasa |
|---|---|
| Manchester City | 19 |
| Bayern Munich | 18 |
| Arsenal | 17 |
| Paris Saint-Germain | 17 |
| Barcelona | 15 |
| Crystal Palace | 12 |
| Manchester United | 12 |
| Al-Hilal | 12 |
| Atletico Madrid | 12 |
| Liverpool | 11 |
| Borussia Dortmund | 11 |
| Galatasaray | 11 |
| Slavia Prague | 10 |
| AC Milan | 10 |
| PSV Eindhoven | 10 |
| Real Madrid | 10 |
| Fenerbahce | 10 |
Kasancewar Manchester City ce keda mafi yawan wakilai a gasar yana nuna irin tasirin da kungiyar ke da shi a kwallon kafa ta duniya. Haka kuma kasancewar kungiyoyi irin su Barcelona, Bayern Munich, Arsenal da PSG a saman jerin ya kara tabbatar da cewa har yanzu su ne cibiyoyin da ke tara fitattun ‘yan wasan duniya.
Yayin da ake sa ran gasar FIFA World Cup 2026 za ta kasance mafi girma a tarihi da kungiyoyi 48, magoya baya za su yi anfani da damar ganin taurarin da suke kallo a matakin kungiya suna fafatawa domin daukaka kasashensu.
Domin karin labaran gasar kofin duniya da tarihin fitattun yan wasa, duba Tarihin Andrés Iniesta.
Haka kuma za ka iya karanta karin bayanai game da gasar FIFA World Cup a Wikipedia.








