eFootball Kick-Off Ya Kaddamar A Nintendo Switch 2 Tare Da Sabbin Fasaloli

eFootball Kick-Off ya zama sabon wasan ƙwallon ƙafa da kamfanin Konami ya ƙaddamar a kan Nintendo Switch 2. Wannan sabon sigar daga jerin wasannin eFootball, wanda a baya aka fi sani da PES (Pro Evolution Soccer), ya zo da sabbin abubuwa da hanyoyin wasa da za su bai wa masoya ƙwallon ƙafa damar jin daɗin wasa a ko’ina da kowane lokaci.
Konami ta sanar da ƙaddamar da eFootball Kick-Off a ranar 3 ga Yuni, 2026, inda wasan ya haɗa manyan ƙungiyoyi da ƙasashe daga sassa daban-daban na duniya. Haka kuma, yan wasa zasu iya amfani da fitattun taurarin zamani da kuma tsoffin gwarazan ƙwallon ƙafa.
Sabbin Hanyoyin Wasa A eFootball Kick-Off
Sabon wasan yazo da wasu hanyoyin wasa na musamman da ba a samu a sauran sigogin eFootball ba.
International Cup
Wannan yanayin wasa yana bai wa masu wasa damar jagorantar ƙasarsu a gasar ƙasashen duniya mafi girma, tare da fafatawa domin lashe kambun duniya.
World Tour
A wannan yanayin, za ka iya gina ƙungiyarka daga tushe sannan ka shiga gasa a sassa daban-daban na duniya. Ana samun damar ɗaukar sabbin yan wasa bayan cin nasara ko kuma ta amfani da Coins domin siyan fitattun taurari.
Wall Ball
Wasan mutum uku da mutum uku ne a filin da ke kewaye da bango. Ƙungiyar da ta fara zura ƙwallaye biyar ita ce za ta yi nasara.
Obstacle Race
Wannan ƙaramin wasa ne da ke gwada ƙwarewar dribbling, inda yan wasa zasu kauce wa cikas daban-daban domin samun mafi yawan maki.
Takefusa Kubo Da Lionel Messi Sun Bayyana A Tallan Wasan
Domin murnar ƙaddamar da eFootball Kick-Off, Konami ta fitar da sabon bidiyon talla wanda ya nuna tauraron Japan Takefusa Kubo. Haka kuma an fitar da wani gajeren bidiyo da ke nuna Lionel Messi da wasu fitattun taurari suna jin daɗin wasan cikin yanayi mai sauƙi.
Kyautar Roberto Carlos Ga Masu Siyan Wasan
Duk wanda ya sayi eFootball Kick-Off zai samu tsohon gwarzon Brazil Roberto Carlos a matsayin kyauta domin amfani da shi a eFootball Mobile na Android da iOS.
Menene eFootball Kick-Off?
eFootball Kick-Off shi ne sabon wasan ƙwallon ƙafa na farko da aka ƙera musamman domin Nintendo Switch 2. Wasan yana cikin jerin eFootball wanda ya maye gurbin tsohon PES.
Masu wasa zasu iya jin daɗin hanyoyi daban-daban kamar World Tour, International Cup da kuma wasu nau’ikan wasannin ƙwallon ƙafa masu sauƙi. Haka kuma an tsara tsarin sarrafa wasan ta yadda sabbin masu wasa za su iya koyon wasa cikin sauƙi.
Game Da Kamfanin Konami
Kamfanin Konami ya fara aiki ne a shekarar 1973, kuma ya zama ɗaya daga cikin manyan kamfanonin wasanni na duniya. A yau, Konami na samar da shahararrun wasanni kamar eFootball, Metal Gear, Silent Hill, Castlevania, Contra da kuma Yu-Gi-Oh!.








