Sharhi

Jerin Mafi Kwarewa Wajen Dribbling A Turai 2025-26: Lamine Yamal Ya Zarce Kowa

Dribbling yana daga cikin abubuwan da suka fi kayatar da magoya bayan ƙwallon ƙafa a duniya. Duk lokacin da ɗan wasa ya rika wuce abokan hamayya cikin sauƙi, hakan na tayar da hankali da nishadi a filin wasa.

A kakar 2025-26, manyan yan wasa daga kungiyoyi irin su FC Barcelona, Real Madrid da Manchester City sun nuna bajinta sosai wajen dribbling.

Ga jerin yan wasan da suka fi kowa successful dribbles a manyan leagues biyar na Turai wato Premier League, La Liga, Serie A, Bundesliga da Ligue 1.

10. Nico Paz – Dribbles 69

Dan wasan Argentina Nico Paz ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa Como samun tikitin Champions League.

Duk da rade-radin komawarsa Real Madrid, Paz ya bayyana cewa hankali yake mayarwa wajen taimaka wa kungiyarsa ta yanzu.

9. Iliman Ndiaye – Dribbles 69

Tauraron Everton ya nuna bajinta sosai a Premier League.

Ndiaye yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka fi kwarewa wajen kai hari da dribbling a Ingila a kakar bana.

8. Victor Munoz – Dribbles 75

Matashin dan wasan Osasuna ya fara daukar hankalin masu bibiyar ƙwallon ƙafa a Spain.

Duk da yawan failed dribbles dinsa, Victor Munoz yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka fi kokarin kai hari a La Liga.

7. Kylian Mbappe – Dribbles 77

Kylian Mbappe yana cigaba da amfani da gudunsa wajen tsoratar da masu tsaron baya.

Duk da cewa baya yawan shiga cikin ƙananan spaces kamar sauran wingers, saurin da yake da shi na sa ya zama mai wahalar tsayawa.

6. Yann Gboho – Dribbles 77

Dan wasan Toulouse ya kasance daya daga cikin abubuwan mamaki a Ligue 1.

Rahotanni sun nuna cewa yana iya wakiltar Ivory Coast a nan gaba, wanda zai kara wa kasar karfi a World Cup 2026.

5. Kenan Yildiz – Dribbles 78

Tauraron Juventus yana daya daga cikin mafi kayatarwa a Serie A.

Kenan Yildiz ya nuna cewa yana da babban makoma saboda yadda yake iya wuce ‘yan wasa cikin sauƙi.

4. Jeremy Doku – Dribbles 82

Manchester City na ci gaba da more bajintar Jeremy Doku.

Dan wasan Belgium din ya zama mafi yawan successful dribbler a Premier League a wannan kakar.

Gudunsa da agility dinsa suna sa ya zama daya daga cikin mafi haɗari a Turai.

3. Vinicius Junior – Dribbles 87

Vinicius Junior yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka fi yawan kokarin dribbling a duniya.

Duk da cewa yana yawan rasa ƙwallo a wasu lokuta, hakan baya hana shi sake gwadawa.

Wannan jarumta ce ta sa ya zama daya daga cikin mafi hatsari a Real Madrid.

2. Yan Diomande – Dribbles 118

Matashin dan wasan Ivory Coast yana daya daga cikin biggest breakout stars na kakar 2025-26.

Kungiyoyi irin su Barcelona da Liverpool sun fara nuna sha’awar daukar sa.

Yan Diomande ya zama daya daga cikin ‘yan wasa biyu kacal da suka haura successful dribbles 100 a Turai.

1. Lamine Yamal – Dribbles 133

Lamine Yamal shi ne sarkin dribbling a Turai a kakar 2025-26.

Matashin dan wasan Barcelona ya zarce kowa da successful dribbles 133, abin da ya nuna irin hazakar da yake da ita duk da kasancewarsa mai shekaru 18 kacal.

Yamal ya ci gaba daga inda ya tsaya a kakar da ta gabata, inda ya kasance daya daga cikin mafi kayatarwa a duniya.

Mutane da dama suna kwatanta shi da tsofaffin taurari irin su Lionel Messi da Neymar saboda yadda yake wuce ‘yan wasa cikin sauƙi.

Duk da cewa ya samu injury da ya kawo karshen kakarsa a watan Afrilu, har yanzu babu wanda ya kusa kaiwa lambobinsa.

Kammalawa

Kakar 2025-26 ta nuna cewa akwai sababbin taurari masu iya dribbling a Turai.

Daga Vinicius Junior zuwa Jeremy Doku da Kenan Yildiz, magoya baya sun ga abubuwa masu kayatarwa sosai.

Amma babu shakka, Lamine Yamal ne ya fi kowa haskawa a bangaren dribbling a duniya yanzu.

Leave a Reply

Related Articles