La Liga Ta Kulla Sabon Yarjejeniyar TV Sama Da €1bn A Shekara, Real Madrid Taƙi Amincewa

La Liga ta kulla wata sabuwar yarjejeniyar talabijin ta cikin gida da kamfanonin Telefónica da DAZN, kuma wannan sabon kwantiragi ya zarce €1 biliyan a kowace shekara, a cewar rahoton MARCA.
Wannan haƙƙin na TV zai haɗa La Liga EA Sports daga kakar 2027-28 zuwa 2031-32, inda jimillar kuɗin yarjejeniyar ya kai €5.25 biliyan, wanda ya karu daga €4.95 biliyan na kwangilar baya.
Idan aka haɗa da sauran bangarori kamar:
HORECA (€650m)
La Liga Hypermotion (€175m)
Free-to-air rights (€60m)
Jimillar ta haura €6.135 biliyan, wanda ke nuni da kashi 9% na ƙaruwa gaba ɗaya.
Haƙƙin HORECA ya ƙaru da 30%, yayin da La Liga Hypermotion ya tashi da 40%.
Masu watsa shirye-shirye za su ci gaba da tsarin 5 da 5 a kowanne mako, amma ikon Movistar na mallakar cikakkun wasanni uku a makonni dabam-dabam zai ƙare.
A zaben da aka yi kan wannan sabon kwangila, Barcelona, Atletico Madrid, da Osasuna sun goyi bayan yarjejeniyar.
Sai dai Real Madrid ta kada kuri’ar ƙin amincewa.
Atletico Madrid ta taya La Liga murna bisa cimma yarjejeniyar.
Shugaban La Liga, Javier Tebas, ya bayyana wannan sabon kwantiragi a matsayin labari mai kyau sosai wajen tabbatar da kwanciyar kuɗin gasar.
Ya ce samun ƙaruwa a irin wannan lokaci da tattalin arziki ke faman durkushewa a duniya, yana nuna ƙarfi da ƙimar gasar La Liga.
La Liga ta danganta wannan nasara da:
ƙirƙira da cigaban fasaha,
matakan yaƙi da fashin TV (anti-piracy),
da shirin da suka yi tun da wuri kan sabon tsarin UEFA.








