Labarin Wasanni

Makomar Cristiano Ronaldo Na Fuskantar Barazana A Saudi Arabia Saboda Rikicin Kuɗaɗe

Makomar Cristiano Ronaldo a gasar Saudi Pro League na cikin shakku, yayin da rahotanni ke nuna cewa yana cikin rikici da shugabannin kwallon kafa na Saudi Arabia, sakamakon rashin gamsuwarsa da irin tallafin kuɗi da kulob ɗinsa Al Nassr ke samu idan aka kwatanta da manyan abokan hamayya kamar Al Hilal.

‎‎Rahotanni sun bayyana cewa jami’an kwallon kafa na Saudi Arabia na rasa haƙuri da Ronaldo, yayin da ɗan wasan ke tunanin ci gaba da yajin aiki na buga wasa (strike) ta hanyar ƙin fitowa wasa duk da cewa yana cikin koshin lafiya kuma yana atisaye tare da takwarorinsa.

‎‎Yajin Aikin Ronaldo Na Iya Lalata Sunan Saudi Pro League

‎‎A cewar bayanai, wannan matakin da Ronaldo ke ɗauka yana barazana ga martabar Saudi Pro League (SPL) da kuma Public Investment Fund (PIF) asusun jari na gwamnatin Saudi Arabia wanda ke da rinjaye a kulob ɗin

  • ‎‎Al Nassr
  • ‎Al Hilal
  • ‎‎Al Ahli
  • ‎‎Al Ittihad

‎‎Jami’an SPL na ƙoƙarin tabbatar da cewa Ronaldo ya dawo fili wasa a ranar Juma’a, inda suka yi masa gargadi a fili, suna mai cewa rashin buga wasa na iya shafar hoton gasar a idon duniya.

‎Ronaldo Na Jin Al Hilal Na Samun Fifiko

‎‎Rahotanni sun nuna cewa Cristiano Ronaldo na da yakinin cewa Al Hilal na samun fifiko wajen tallafin kuɗi daga PIF, fiye da Al Nassr. Wannan ne ya sa ya nuna ɓacin rai, musamman bayan Al Hilal sun ƙara ƙarfafa tawagarsu a kasuwar canjin yan wasa ta watan Janairu.

‎Daga cikin manyan yan wasan da Al Hilal suka ɗauka akwai Karim Benzema, wanda ya fara wasa da ƙarfi sosai, inda ya zura kwallaye uku (hat-trick) a wasansa na farko, yayin da Al Hilal suka doke Al Akhdoud da ci 6–0.

‎‎Wannan nasara ta sa Al Hilal suka ƙara tazara tsakaninsu da Al Nassr zuwa maki huɗu a teburin gasar.

‎‎Me Ya Sa Wannan Ya Fusata Ronaldo?

‎‎Ronaldo ya yi imanin cewa

‎Al Nassr ba sa samun irin kuɗin tallafi da sauran kulob ɗin PIF

‎‎Al Hilal na samun manyan yan wasa cikin sauƙi

‎‎Wannan ya rage damar Al Nassr na lashe gasar

‎‎Ko da yake Ronaldo ya wallafa hotonsa yana atisaye a shafin X (Twitter), inda aka sa ran zai buga wasa da Al Ittihad, har yanzu akwai shakku ko zai fito fili.

‎Jami’ai Sun Roki Ronaldo Ya Dawo Fagen Wasa

‎‎Wani babban jami’i ya bayyana cewa:

‎‎Masoya a Saudi Arabia da kuma ko’ina a duniya suna son ganin Cristiano Ronaldo ya dawo yana wasa da fafatawa. Tallafin da aka ba shi tun zuwansa ƙasar nan yana nan daram, kuma har yanzu akwai abubuwa da dama da za a iya cimmawa.

‎‎Duk da cewa Ronaldo na samun albashi da ake kiyasta fam £500,000 a rana, jami’ai sun nuna mamakin yadda har yanzu yake nuna rashin jin daɗi.

‎Sharuddan Kwantiragin Ronaldo Da Halin Da Ake Ciki

‎Ronaldo na da watanni 18 a kwantiraginsa da Al Nassr

‎‎Akwai kudin fansa na fam £43m (€50m) a lokacin bazara

‎‎Duk da cewa ya cika shekara 41, har yanzu yana ɗaya daga cikin fitattun yan wasa a gasar

‎‎Abin lura shi ne cewa Al Nassr na da damar hawa saman teburin Saudi Pro League idan suka yi nasara a wasansu na gaba abin da jami’ai ke fatan zai ja hankalin Ronaldo ya dawo fili.

‎‎Rikici Na Ci Gaba Tsakanin Ronaldo Da Al Nassr

‎Cristiano Ronaldo bai buga wasan da Al Nassr suka doke Al Riyadh a ranar Litinin ba, kuma majiyoyi sun tabbatar da cewa yana cikin rashin jin daɗi game da yadda ake tafiyar da kulob ɗin.

‎‎A ganinsa, Al Nassr ba sa samun adalci wajen rabon kuɗin tallafi idan aka kwatanta da sauran kulob ɗin da PIF ke da su.

Leave a Reply

Related Articles