Albashin Victor Osimhen Ya Isa Ya Gina Cikakkiyar Ƙungiya A Galatasaray

Galatasaray taci gaba da jan hankali a duniya saboda ɗaukar ɗan wasan ƙasa da ƙasa na Najeriya Victor Osimhen. A wani bayani da mai horar da ƙungiyar, Okan Buruk, yayi kwanan nan, ya bayyana cewa albashin Osimhen kadai zai iya gina cikakkiyar ƙungiya.
Dalilin furucin Buruk
A lokacin da yake hira bayan nasarar Galatasaray da Istanbulspor 3-1 a gasar Turkish Cup, Buruk ya bayyana cewa:
Kudin sayan ɗan wasan da albashin Osimhen sun karu sosai tun daga bara. Idan kana kallon albashin Osimhen, da shi kadai za ka iya gina cikakkiyar ƙungiya.
Mai horarwar yaci gaba da cewa
Mun kawo wasu yan wasa masu muhimmanci sosai kamar Singo, Uğurcan, Sané, da İlkay. Kowace ƙungiya tana da kasafin kuɗinta, kuma lokacin da ka tsara kasafin shekara-shekara, dole ne abi shi sosai.
Buruk ya bayyana cewa albashin Osimhen da kudin sayansa sun sa an samu ƙaruwa mai yawa a kashe kudaden ƙungiya a bara da kuma wannan kakar, kuma yana buƙatar kulawa wajen tsara kasafin gaba ɗaya.
Albashin Victor Osimhen da kudin sayen shi
Victor Osimhen ya bar Napoli bayan shekaru biyar, lokacin da Galatasaray ta biya €75 miliyan don sayan ɗan wasan daga ƙungiyar Italiya.
- Albashin shekara-shekara: €15 miliyan
- Bonus: €1 miliyan a kowace shekara
- Kudin hoto (image rights): €5 miliyan a kowace shekara
- Tsawon kwangila: shekaru 4
Jimillar kuɗin da Galatasaray zata kashe a kansa a tsawon kwangilar ta kai kimanin €159 miliyan. Wannan ya haɗa da kudin sayen ɗan wasan da albashin sa, wanda Buruk yace zai iya gina cikakkiyar ƙungiya daga kansa.
Tasirin Osimhen ga Galatasaray
Osimhen ya buga kakar wasa mai ƙarfi a matsayin ɗan aro daga Napoli kafin a saye shi a hukumance. Duk da cewa wasu manyan ƙungiyoyi daga Premier League da Saudi Arabia suna sha’awar ɗan wasan, Galatasaray taci nasara wajen kawo shi Istanbul.
Mai horarwa Okan Buruk ya nuna cewa ɗaukar Osimhen da sauran ƴan wasa masu muhimmanci ya taimaka wajen karfafa tawagar da kuma inganta ƙungiyar gaba ɗaya.
Mun kawo yan wasa masu muhimmanci waɗanda zasu taimaka ƙungiyar sosai, kuma wannan wani mataki ne na tsara kungiyar da kyau don cimma nasarori a kakar wasa. Inji Buruk
Shirin su na gaba wasa da Rizespor a Super Lig
Tunda Galatasaray na fuskantar Rizespor a wasan Super Lig mai zuwa, Buruk ya yanke shawarar baiwa Osimhen hutu daga wasan Istanbulspor a ranar Laraba don tabbatar da lafiyar ɗan wasan da kuma shirye-shiryen tawagar gaba.
Buruk ya bayyana cewa
Mun yanke shawarar barin Osimhen ya huta a wannan wasan don ya samu kuzari kafin mu fuskanci Rizespor a gaba. Wannan yana cikin tsare-tsaren mu na tabbatar da lafiyar yan wasa da nasarar tawaga.
Furucin Okan Buruk ya nuna cewa Victor Osimhen na ɗaya daga cikin manyan ɗan wasan da Galatasaray ke da su, kuma albashinsa da kudin sayansa sun nuna irin tasirin da ɗan wasan ke da shi a ƙungiya. Tare da sauran ‘yan wasa kamar Singo, Uğurcan, Sané, da İlkay, Galatasaray na da burin yin gasa mai ƙarfi a duk gasar da take shiga a kakar nan.








