Labarin Wasanni

Laporta Yayi Bankwana Da Yan Wasan Barcelona, Hansi Flick Ya Nuna Goyon Baya

Shugaban ƙungiyar FC Barcelona, Joan Laporta, ya sanar da murabus dinsa a hukumance a ranar Litinin domin ya ba kansa damar tsayawa takarar sake zama shugaban kulob ɗin a zaɓen da ke tafe.

‎‎Bayan murabus ɗinsa, Rafa Yuste ya karɓi ragamar shugabancin ƙungiyar a matsayin shugaban rikon ƙwarya, wanda zai ci gaba da tafiyar da al’amuran kulob ɗin har sai an kammala zaɓen sabon shugaba.

‎‎Laporta ya ziyarci dakin sauya kaya

‎‎Saboda ranar hutun yan wasa ce, Laporta bai samu damar yin bankwana da yan wasan Barcelona a ranar murabus ɗinsa ba. Sai dai a ranar Talata ne ya je Cibiyar Horarwa ta Ciutat Esportiva domin yin bankwana da koci Hansi Flick da kuma yan wasan ƙungiyar.

‎‎Laporta ya isa cibiyar horon da misalin ƙarfe 9:20 na safe, tare da mai ba shi shawara kuma mamba a kwamitin wasanni, Enric Masip. Shugaban rikon ƙwarya, Rafa Yuste, shima ya iso daga baya.

‎‎Tsohon shugaban yayi amfani da wannan damar ne domin ya gaishe da yan wasa da ma’aikatan horaswa cikin natsuwa kafin fara atisayen rana da aka shirya da ƙarfe 11:00 na safe, yayin da Barcelona ke ci gaba da shirin fafatawa da Atletico Madrid a wasan farko na kusa da na ƙarshe na Copa del Rey.

‎‎Dangantaka ta musamman da yan wasa

‎‎Laporta ya shahara wajen kusantar yan wasa da dakin sauya kaya a tsawon lokacin da yake shugabancin Barcelona. Ziyarar sa zuwa cibiyar horo abu ne da ya zama ruwan dare, musamman domin nuna goyon baya ga koci da yan wasa a lokutan nasara da kuma lokacin ƙalubale.

‎‎Wannan mataki na nuna yadda yake da cikakkiyar amincewa da aikin da Hansi Flick da tawagarsa ke yi a kulob ɗin.

‎Shirin dawowa shugabanci

‎Daga yanzu, Laporta ya koma matsayin ɗan takara kamar sauran masu neman shugabanci. Zai fara tattara sa-hannun mambobin kulob ɗin domin cika sharuddan da doka ta tanada, da burin sake zama shugaban Barcelona daga ranar 30 ga Yuni mai zuwa.

‎‎Rahotanni sun nuna cewa Laporta ya bar saƙo mai ƙarfafa gwiwa ga yan wasa da ma’aikata inda yace

‎‎Za mu sake haɗuwa nan ba da jimawa ba, zan yi nasara, kamar yadda ɗan jarida Javi Miguel na AS ya rawaito.

‎‎Flick ya mara wa Laporta ba

A cikin dakin sauya kaya kuwa, koci Hansi Flick ya bayyana goyon bayansa ga shirin Laporta na dawo wa shugabanci, tare da Deco a matsayin daraktan wasanni, domin tabbatar da kwanciyar hankali da daidaito a kulob ɗin.

‎Ba sabon abu ba ne ganin kyakkyawar alaƙa tsakanin Flick da Laporta, inda kocin ɗan Jamus din ke ganin tsohon shugaban a matsayin mutumin da zai iya ci gaba da gina makomar Barcelona.

Leave a Reply

Related Articles