Tarihin Messi: Rayuwar Fitaccen Dan Wasa Lionel Messi

Lionel Andrés Messi, Wani Suna Ne Wanda Tarihin Kwallon Kafa (Football) Baya Cika Ba Tare Da An Ambato Sunansa Ba. An Haife Shi Ne A Ranar 24 Ga Yuni, 1987, A Rosario, Argentina, Rayuwarsa Labari Ne Mai Cike Da Jarumtaka Da Kuma Juriya A Kan Kalubale. A Yau Mun Kawo Muku Cikakken Tarihin Messi Daga Farkon Sa Har Izuwa Zuwa Yanzu.
Farkon Tarihin Messi: Rayuwa Da Kalubale

Farkon Rayuwar Lionel Messi Ya Kasance Yana Da Sha’awar Kwallon Kafa, Sai Dai Kuma Bashida Tabbas (Uncertainty). Ya Fara Buga Wasa A Kungiyar Grandoli, Sa’annan Daga Baya Ya Koma Newell’s Old Boys, Inda A Lokacin Ya Nunawa Duniya Baiwarsa.
Sai Dai, Kalubalen Sa Na Farko Ba Ya Da Alaƙa Da Wasan Kwallon Kafa, Yana Da Alaka Ne Da Lafiyar Sa. Lokacin Yana Dan Shekara 11, An Same Shi Da Cuta Mai Hana Girman Jiki (Growth Hormone Deficiency – GHD).
Wata Cutace Da Ke Bukatar Jinya Kuma Da Tsada Sossai. Babu Wani Kulob Ko Wadanda Ke Da Halin Biyan Kuɗin Allurar Hormones Da Za’a Ringa Yi Masa Na Wata-Wata, Wannan Ya Sanya Makomar Sa Cikin Hatsari.
Komawar Messi Barcelona
Makomar Messi Ta Sauya A Shekarar 2000 Lokacin Da Ya Yi Gwaji (Trial) A FC Barcelona. Daraktan Wasanni Na Lokacin, Wato Carles Rexach, Yana Son Messi Sosai, Musamman Saboda Kwarewarsa.
A Wannan Lokacin Ne Aka Yi Wata Yarjejeniya Ta Musamman Da Ta Shiga Tarihi: A Ranar 14 Ga Disamba, 2000, A Wani Wuri Na Barcelona Tennis Club, Rexach Bai Sami Wata Takarda Ba, Saboda Haka Ya Rubuta Yarjejeniyar Farko A Kan Wani Napkin, Inda Ya Amince Barcelona Zata Dauki Nauyin Kudin Jinyyar Messi.
Wannan Yasa Messi Ya Shiga La Masia, Wato Sanannen Cibiyar Horar Da Matasa Ta Barcelona (Academy). Nan Da Nan Ya Zama Jagora A Bangaren, Sa’annan Kuma Ya Fara Buga Wasa A Babban Ƙungiyar Barcelona Yana Ɗan Shekara 17 A Shekarar 2004.
Zamanin Golden: Lokacin Da Messi Sukayi Tasiri A Duniya

Zamanin Pep Guardiola (2008-2012) Shine Lokacin Da Messi Ya Zama Gwarzon Duniya Kuma Shugaba A Wasan Kwallon Kafa, A Lokacin Babu Mai Daga Musu Yatsa. A Lokacin Shine “False Nine“.
Inda Barcelona Ta Zama Ƙungiya Mafi Ban Tsoro A Duniya. A Lokacin Sun Lashe Kofuna Shida Cikin Shekara Ɗaya A Shekarar 2009, Record Din Da Ya Baiwa Duniya Mamaki. Kai Bai Baka Ba?
A Shekarunsa Da Yayi A Barcelona, Ya Kafa Records Da Yawa Da Ba Za A Iya Karya Su Ba:
- Mafi Yawan Wanda Ya Ci Kwallaye A Tarihin Barcelona Da Kuma La Liga.
- Ya Lashe Ballon d’Or Mafi Girma Har Sau Bakwai (Kafin Ya Lashe Na Takwas Daga Baya).
Wannan Nasara Tashi, Taci Gaba Har iZuwa Shekarar 2021 Lokacin Da Matsalar Kuɗi Da Ƙa’idojin La Liga Suka Tilasta Masa Barin Ƙungiyar Da Ya Fara Rayuwarsa Da Ita (Barcelona). Barin Sa Ya Kasance Abin Tausayi Ga Masoyan Kwallon Kafa A Duniya.
Nasarorin Ƙasa Da Kofin Duniya (The GOAT Debate)

Duk Da Nasarar Da Ya Samu A Barcelona, Mutane Suna Cewa Messi Ba Zai Taba Zama GOAT Ba Wato Greatest Of All Time, Har Sai Ya Lashe Babban Kofin Kasar Sa.
Wannan Tattaunawa Ta Dau Zafi, Inda Kowa Yake Ganin Cewa Matukar Ya Cika Da Zai Iya Cinma Kasarsa Kofin Duniya: Sai Kuma Labari Ya Sauya:
- Copa América (2021): Ya Jagoranci Argentina Lashe Copa América A Brazil.
- FIFA World Cup Qatar (2022): A Nan Ne Ya Cikasa Tarihin Sa Gaba Daya.
Ya Ci Kofin Duniya, Dama Itace Record Da Ta Rage Masa Kacal. Wannan Nasarar Ta Sa Masu Magana A Kan Zamansa GOAT Suka Yi Shiru. Inda Mutane Da Yawa Suka Ɗauke Shi A Matsayin Na Musamman, Sai Dai Yan Adawa Sun Ci Gaba Da Sukarsa.
Dukiya Da Adadin Kudin Messi (Net Worth)

Lionel Messi Yana Daga Cikin ‘Yan Wasa Mafi Arziki A Duniya. Duk Da Albashinsa Ya Gaza Kan Na Abokin Takararsa Wato Cristiano Ronaldo, Amma Kimar Sa Ta Dukiya (Net Worth) Tana Da Yawa Sosai Saboda Yarjejeniyar Sa Da Sponsors Da Kuma Hannun Jarinsa A Kasuwanci.
- Ƙididdigar Dukiya: Wasanni Ta Kididdige Dukiyar Messi Ya Kai $600 Miliyan (Dala Miliyan 600).
- Manyan Hanyoyin Shigar Kudinsa: Yana Samun Manyan Kuɗin Shiga Daga Kamfanin Adidas, Da Pepsi, Da Kuma Yarjejeniyar Sa Ta MLS Wanda Ya Haɗa Da Kasuwa Daga Apple TV Da Adidas Ga Hukumar MLS.
Lionel Messi Family Da Yaransa
Rayuwar Messi Ta Sirri Tana Da Tsafta Kuma Inganci. Dan Wasa Ne Da Aka San Shi Da Kulawa Da Iyalansa (Family Man).
- Matarsa: Ya Auri Matarsa Tun Yana Yaro, Wato Antonela Roccuzzo, A Shekarar 2017. Suna Da Tarihin Soyayya Tun Suna Ƙanana A Rosario.
- Yara: Suna Da Yara Maza Uku: Thiago, Mateo, Da Kuma Ciro. Sun Fifita Rayuwar Sirri (Private Life) Sossai.
Rayuwar Messi A Amurka: Kungiyar MLS
A Shekarar 2023, Ya Koma Inter Miami, A Major League Soccer (MLS) Ta Amurka. Tasirinsa A Gasar MLS Ya Sauya Nan Take. Ya Karawa League Din Yawan Masu Kallo Da Kudin Shiga Na Wasan Kwallon Kafa A Amurka.
Tarihin Messi Ba Labari Ne Na Kwallon Kafa Ba Kawai, Labari Ne Na Cin Nasara A Kan Kalubale, Kulawa Ga Iyali, Da Kuma Juriya Har Ka Cimma Abinda Duniya Take Tunanin Ba Zaka Taba Iyawa Ba, Kuma A Cikin Sanyi.
Kasance Da Wasanni, Domin Karanta Tarihin Kwallon Kafa Da Na Yan Wasa Gabadaya.






