Beckham Na Fatan Hada Ronaldo Da Messi A Inter Miami, Yayin Da Rikici Ke Ƙara Ƙamari A Al-Nassr

Tsohon tauraron ƙwallon ƙafa kuma mai kula da Inter Miami, David Beckham, yanada burin kafa wani tarihi a duniyar kwallon ƙafa ta hanyar haɗa Cristiano Ronaldo da Lionel Messi a kungiya guda, Inter Miami a lokacin kasuwar saye da sayarwa ta bazara mai zuwa, a cewar rahotanni daga Turai.
Idan hakan ta tabbata, zai kasance karo na farko da manyan taurarin biyu zasu taka leda tare a kulob ɗaya, lamarin da zai zama abin tunawa a tarihin kwallon ƙafa na duniya.
Tarihin Tafiyar Ronaldo Zuwa Saudi Arabia
Cristiano Ronaldo ya bar Manchester United a ƙarshen shekarar 2022 bayan samun rikici mai zafi tsakaninsa da kocin kungiyar a wancan lokaci, Erik ten Hag.
Rikicin ya kai kololuwa ne bayan wata fitacciyar hira da Ronaldo yayi da Piers Morgan, wadda ta janyo soke kwantaraginsa da kungiyar ta hanyar fahimtar juna.
Bayan haka, Ronaldo yaƙi tayin dawowa Turai, inda ya koma Al-Nassr ta kasar Saudi Arabia a farkon 2023. Tun bayan isowarsa, ya nuna bajinta sosai, inda ya ci kwallaye 117 a wasanni 133, adadi mai nuna cewa har yanzu yana cikin manyan yan wasan duniya duk da shekarunsa.
Rashin Jin Dadin Ronaldo a Al-Nassr
Duk da yawan kwallayen da yake ci, an ruwaito cewa Ronaldo bai gamsu da halin da Al-Nassr ke ciki ba, musamman bayan sun kare gasar Saudi Pro League a matsayi na uku, tare da ficewa daga gasar AFC Champions League a matakin daf da karshe.
A cikin yan makonnin nan, dan wasan mai shekaru 40 ya shiga wani irin yajin aiki (strike), inda bai buga wasanni biyu na karshe na Al-Nassr ba, duk da cewa yana cikin koshin lafiya. Rahotanni sun nuna cewa rashin jin dadinsa ya shafi yadda Saudi Public Investment Fund (PIF) ke tallafa wa Al-Nassr, idan aka kwatanta da sauran kungiyoyin da suke karkashinsa.
Al-Hilal Na Kara Karfi, Al-Nassr Na Kallo
Daya daga cikin manyan dalilan fushin Ronaldo shi ne yadda abokan hamayyar Al-Nassr, wato Al-Hilal, suka samu damar ɗaukar taurari masu yawa, ciki har da Karim Benzema daga Al-Ittihad a kasuwar hunturu.
A gefe guda kuma, Al-Nassr ta samu sabbin yan wasa kalilan kacal, ciki har da
- Hayer Abdulkareem, dan wasan tsakiya daga Iraki mai shekaru 21
- Abdullah Al-Hamdan, dan wasan gaba daga Saudi Arabia
Wannan bambanci ya karfafa kungiyoyi ya kara janyo tambayoyi kan adalcin rabon tallafi daga PIF.
Inter Miami da Shirin Tarihi na Beckham
A cewar shafin wasanni na Spain, Fichajes, Inter Miami na son ci gaba da gina sunanta a fagen kwallon ƙafa na duniya, kuma ɗaukar Cristiano Ronaldo zai kasance babban mataki a wannan buri.
Rahoton ya bayyana cewa
Beckham shi ne mai tsara wannan mafarki
Ya riga ya shawo kan Lionel Messi ya koma MLS
Yanzu yana ganin zuwan Ronaldo zai zama cikakken kammala aikin da ya fara a Amurka
Idan Ronaldo ya koma Inter Miami, zai hada shi da Messi a kungiya guda, abin da masoya kwallon ƙafa a duniya ke kallon a matsayin wani tarihi da ba a taba ganin irinsa ba.
Rikici da Sukar Ronaldo a Saudi Arabia
Duk da haka, ba kowa ke maraba da halayen Ronaldo a Saudi Arabia ba. Fitaccen mai sharhi a gasar Saudi Pro League, Walid Al-Faraj, ya fito fili yana sukar tauraron dan wasan.
Yace Cristiano Ronaldo yana bukatar ya san matsayinsa. Wannan kasa ana kiranta Saudi Arabia, ba Ronaldo’s Arabia ba. Yana rikita matsayin jakada dana manaja. Shi ma’aikaci ne da ke karbar albashi mai yawa, kuma dole ne ya girmama gasar, ko kuma yabar ta.
Wannan magana ta kara bayyana cewa dangantaka tsakanin Ronaldo da masu ruwa da tsaki a Saudi Arabia na iya kara tabarbarewa idan ba a samu maslaha ba.
Me Zai Biyo Baya?
Duk da cewa Ronaldo ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi da Al-Nassr har zuwa Yuni 2027, wanda ake cewa zai iya kai darajar fam miliyan 492, akwai kuma sashe na sakin kwantiragi da ya kai kusan fam miliyan 43 a bazara.
Wannan na nufin duk wata yiwuwar komawarsa Turai ko Amurka baza ta zama abu mai wuya ba, musamman idan Inter Miami ta yanke shawarar daukar mataki mai karfi.








