Rikicin Ɗaga Tutar Falasdinu Ya Jawo Cece-kuce A Duniya

Wani sabon lamari ya tayar da kura a duniyar ƙwallon ƙafa, bayan FC Barcelona ta fitar da bayani tana nesanta kanta daga ɗan wasanta matashi Lamine Yamal, bayan ya ɗaga tutar Falasdinu a lokacin bikin murnar lashe gasar La Liga a Barcelona.
Lamarin ya faru ne yayin da dubban magoya baya suka taru domin murnar nasarar da Barcelona ta samu a kan Real Madrid da ci 2-0, wanda ya basu kambun gasar La Liga karo na 29.
Barcelona Ta Fitar Da Bayani Ga Masu Goyon Bayanta
A cikin sanarwar da ta fito har da harshen Ibrananci, Barcelona ta bayyana cewa abin da Lamine Yamal yayi ba wani matakin siyasa ba ne daga kungiyar.
Kungiyar tace abin yafaru ne kawai cikin bazata ba tare da wani shiri daga hukumar ko yan wasan ba.
Haka kuma, ta bayyana cewa bidiyon wannan lamari ba za a wallafa shi a kafafen sada zumunta a hukumance ba.
Martanin Isra’ila Da Tashin Hankali
Ministan tsaron Isra’ila ya soki matashin ɗan wasan, inda ya bayyana cewa irin wannan hali na iya haifar da rikici da ƙiyayya a duniya.
Ya kuma yi kira ga Barcelona da ta bayyana matsayinta a fili kan irin wannan lamari, tare da jaddada cewa babu wurin tada fitina ko goyon bayan ayyukan ta’addanci.
Barcelona Ta Jaddada Matsayinta Na Duniya
Kungiyar Barcelona tace tana alfahari da kasancewa kulob ɗin dake wakiltar mutane daga sassa daban-daban na duniya, ciki har da Isra’ilawa da Falasɗinawa.
Ta kuma gode wa magoya bayanta a Isra’ila saboda goyon baya da suke cigaba da bata tsawon shekaru.
Kammalawa
Wannan lamari ya sake nuna yadda ƙwallon ƙafa ke haɗuwa da siyasa a wasu lokuta, musamman idan manyan kulob da fitattun yan wasa kamar Lamine Yamal suka shiga cikin abubuwan da ke tayar da cece-kuce a duniya.








