Tarihi

Jerin Yan Wasa Goma 10, Wanda Sukafi Jimawa A Gasar Zakarun Turai Kuma Suna Cin Kwallo

‎A cewar shafin Transfermarkt, Karim Benzema da Lionel Messi sunyi Shekaru 18 a gasar UEFA Champions League suna zura kwallo a jere, wanda hakan ya sanya su a matsayi na farko a duniya. Cristiano Ronaldo kuwa ya zo na uku da shekaru 16.

‎Jerin yan wasa Goma Na Farko (Top 10):

‎1. Karim Benzema (Lyon, Real Madrid) Shekaru 18 (ya ƙare a 2023)

‎2. Lionel Messi (Barcelona, PSG) Shekaru 18 (ya ƙare a 2023)

‎3. Cristiano Ronaldo (Man United, Real Madrid, Juventus) Shekaru 16 (ya ƙare a 2022)

‎4. Robert Lewandowski (Dortmund, Bayern, Barcelona) Shekaru 14 (daga 2011-12 har yanzu)

‎5. Raúl González (Real Madrid, Schalke) Shekaru 14 (ya ƙare a 2011)

‎6. Antoine Griezmann (Atlético, Barcelona, Atlético) Shekaru 12 (daga 2014-15 har yanzu)

‎7. Didier Drogba (Marseille, Chelsea) Shekaru 12 (ya ƙare a 2015)

‎8. Ryan Giggs (Manchester United) Shekaru 11 (ya ƙare a 2007)

‎9. Kylian Mbappé (Monaco, PSG, Real Madrid) Shekaru 10 (daga 2016-17 har yanzu)

‎10. Sergio Agüero (Atlético, Man City, Barcelona) Shekaru 10 (ya ƙare a 2021)

‎Jerin Wasu da suka kai Kwallaye 10:

‎Thomas Müller, Robin van Persie, Thierry Henry.

‎Wanne ne mafi kyawundan wasan gaba da Champions League ta taɓa gani?

Akwai mutane da yawa suna cewa Ronaldo saboda ya ci gasar sau 5 kuma shine ya fi kowa zura kwallo a tarihinta (140). Wasu kuma suna cewa Messi saboda ya yi shekaru 18 ba tare da ya tsallake ba yana zura kwallo. Benzema ma ya nuna irin wannan bajintar.

‎Shin wani zai iya karya wannan tarihi na shekaru 18?

‎A yanzu Mbappé (shekaru 10) da Lewandowski (14) suna kan hanya mafi kyau. Idan Mbappé ya ci gaba da zura kwallo kowace shekara har zuwa 2033-34, zai iya cimmawa ko kuma ya wuce Messi da Benzema.

Leave a Reply