Romario Yace Yafi Cristiano Ronaldo, Amma Messi Yafi Shi

Tsohon fitaccen ɗan wasan Brazil, Romario, ya sake tayar da muhawara a duniyar ƙwallon ƙafa bayan ya bayyana cewa yafi Cristiano Ronaldo ƙwarewa, amma ya amince cewa Lionel Messi yafi shi.
A wata hira da yayi da LeodiasTV, an tambayi Romario ko yana ganin yafi Cristiano Ronaldo. Cikin ƙarfin gwiwa ya amsa da cewa:
“Eh. Ina ƙasa da Messi, amma ina sama da Cristiano Ronaldo.”
Lokacin da aka tambaye shi dalilin da yasa yake ganin Messi yafi Ronaldo, Romario yace tauraron Argentina yana da baiwar da aka haife shi da ita tun daga farko.
“A ganina Messi mutum ne da aka haifa da wata baiwa ta musamman. Duk abin da yake da shi yanzu, yana tare da shi tun lokacin da aka haife shi,” in ji Romario.
Dangane da Cristiano Ronaldo kuwa, Romario ya bayyana cewa nasarorin da ya samu sun fi danganta da ƙwazo da jajircewa fiye da baiwa ta halitta.
“Cristiano ya zama ɗaya daga cikin manyan ‘yan wasa a duniya ne saboda ƙwarewarsa wajen aiki da kuma ƙwarin gwiwa. Professionalism ɗinsa ne ya kai shi wannan matsayi. Amma idan ana maganar fasaha ta ƙwallo, ba za a iya kwatanta shi da Messi ba,” ya ƙara da cewa.
Romario Ya Zaɓi Fitattun Yan Wasan Tarihi
A wata hira daban, Romario ya bayyana sunayen yan wasan da yake ganin sun fi shi a tarihin ƙwallon ƙafa.
“Pele, Diego Maradona da Messi sun fi ni taka leda. Wataƙila har da Garrincha,” in ji gwarzon da ya taimaka wa Brazil lashe Kofin Duniya na 1994.
Ya kuma bayyana cewa duk da irin girman sunan Cristiano Ronaldo, bai saka shi cikin jerin mafiya kyau a tarihin ƙwallon ƙafa ba.
“Naji Cristiano yana cewa shi ne mafi kyau a tarihin ƙwallon ƙafa. A ganina ba haka bane, amma ina girmama ra’ayinsa. Yana da damar faɗin hakan. Zan iya cewa yana cikin manyan yan gaba guda biyar mafiya kyau,” in ji Romario.
Batun Kwallaye 1,000
Wani abu dake haɗa Romario da Cristiano Ronaldo shi ne batun kaiwa kwallaye 1,000 a rayuwar wasa.
A halin yanzu Ronaldo yana dab da kaiwa wannan tarihi, inda yake da kwallaye sama da 970 a matakin ƙungiyoyi da ƙasa.
Sai dai Romario ya dade yana ikirarin cewa ya riga ya kai kwallaye 1,000 tun a shekarar 2007 lokacin da yake buga wa Vasco da Gama wasa.
Duk da haka, masana da hukumomin ƙwallon ƙafa sun yi jayayya da wannan adadi saboda ya haɗa da wasannin sada zumunci da kuma wasu wasannin da ba na hukuma ba. Bisa bayanan FIFA, Romario yayi ritaya da kwallaye 772 da aka tabbatar a hukumance.
Duk da cece-kucen da ke tattare da wannan batu, kalaman Romario sun sake ƙara zafafa muhawarar da ake yi kan wanda yafi kowa a tarihin ƙwallon ƙafa tsakanin Messi da Cristiano Ronaldo.








