Wanne Dan Wasa Ne Zai Fi Yin Fice A Gasar Premier League Ta Bana? Bukayo Saka, Erling Haaland, Ko Cole Palmer?
Wanene Yafi Tsakanin Pep Guardiola Da Carlo Ancelotti A Dabarun Horarwa?
Guardiola Yana Da Tsari Na Musamman Da Sarrafa Kwallo Wato Tiki-Taka Wanda Ya Sauya Fasalin Kwallon Kafa. Carlo Ancelotti Kuma Yafi Kowa Kwarewa Wajen Sarrafa Manyan 'Yan Wasa Da Samun Nasara A Manyan Wasanni Ba Tare Da Nuna Matsi Ba.
Idan Za Ka Zabi Mai Horarwa Daya Don Ya Gina Kungiyarka Wanene Zai Zama Zabinka?
Wanene Yafi Tsakanin Mohamed Salah Da Bukayo Saka A Gasar Firimiyar Bana?
Salah Yana Ci Gaba Da Nuna Kwarewa Da Kwarewar Da Ya Tara A Shekaru Da Dama A Liverpool. A Daya Bangaren Kuma Saka Yana Nuna Bajinta Da Karfin Matasa A Arsenal.
Tsakanin Kwarewa Da Karfin Kuruciya Wanne Kuke Ganin Zai Fi Tasiri A Wannan Gasar?
Wanene Yafi Tsakanin Erling Haaland Da Kylian Mbappe A Wannan Lokacin?
Idan Aka Duba Yawan Kwallaye Da Kwarewar Zura Kwallo A Raga Haaland Yana Kan Gaba Sosai. Amma Idan Aka Kalli Sarrafa Kwallo Da Taimakawa Abokan Wasa Mbappe Yafi Zama Cikakken Dan Wasa.
Wane Dan Wasa Ne Zai Fi Taimakawa Kungiyarsa Samun Nasarar Lashe Kofin Zakarun Turai A Wannan Kakar?
Lamine Yamal Yana Ɗan Shekara Goma Sha Bakwai Amma Yana Wasa Fiye Da Fitattun 'Yan Wasan Gaba Da Suka Dade Suna Ji Da Kansu. Ku Zuba Ido Ku Kalli Yadda Barcelona Ke Gina Makomar Kwallo.